An yabawa Gidauniya mai zaman kanta ta Farindoki Foundation dangane da ayyukan wanzar da zaman lafiya, cigaba da hadin kai tsakanin al’umma.
Hakimin Billiri da ke ƙaramar hukumar Billiri a jihar Gombe Alhaji Yusuf Muhammad Ali shine ya yi yabon a lokacin da ya hallaci wani babban taro na wasannin motsa jiki da Gidauniyar Farindoki ta shiryawa matasa maza da mata da yara na karshen shekara da a ka kira Run festival.
Hakimin Billirin yace irin wasannin motsa jiki kamartsere,gudun buhu da na ƙwai,da sauran su na taimakawa wajen kara hada kai da kuma motsa jiki wanda ke inganta lafiyar al’umma.
Gidauniyar ta Farindoki ta samu assasawar Barrister Zainab Sabo Mustapha da zummar taimakawa al’umma ta fuskokin dabamdabam.
A jawabinta na godiya ga mahallata taron run festival daya gudana a filin wasa na Billiri, Barrister Zainab ta ce ta shirya taron ne domin kara hadin kai da zaman lafiya tsakanin matasa a Billiri ,inda ta ce baya ga haka an shirya kyauta ta musamman ga dukkanin wadda suka shiga wasannin da aka gudanar, kyautuka da suka hada kudi Naira dubu ɗari biyu ga ko wani ɓangare da yazo na daya tsakanin mata da maza, da Naira dubu ɗari da Hamsin ga na biyu sai dubu dari ga na uku dukkanin su da buhunan masara da wani ɓangare na gidan gonar Farindoki ya bayar.
Da suke nasu jawaban nuna goyon bayan ayyukan Gidauniyar Farindoki Dan majalisar tarraya mai wakiltar mazabar Balanga/Billiri, Ali Isa JC da shugaban karamar hukumar Shangon Fatima Binta Bello sun kara wasu makudan kudade ga wadda su ka yi nasara da kuma waɗanda su ka fafata a gasar