Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya soke ziyarar sa zuwa taron Shugabannin Gwamnatocin Ƙasashe rainon Ingila (Commonwealth (CHOGM) na 2024 a Samoa bayan da wani abu ya bugi jirginsa a Filin Jirgin Sama na JFK a New York, wanda ya lalata gilashin kwalkwalwan jirgin.
Kakakin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana gyara jirgin.A madadinsa, Shugaba Tinubu ya naɗa wata tawagar ministoci, tare da jagorancin Ministan Muhalli, Balarabe Abbas Lawal, don wakiltar Nijeriya a taron.
Taron CHOGM, wanda ya fara ne tun a ranar 21 ga Oktoba, za a kammala shi a ranar 26 ga Oktoba, 2024.