Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Adamawa bayan ta yi watsi da karar da Aishatu Binani ta jam’iyyar APC ta shigar kan rashin cancanta.
A hukuncin da Mai shari’a Tunde Awotoye ya shirya kuma mai shari’a Ebiowei Tobi ya karanta a yau Litinin, Kotun daukaka kara ta kuma bayar da umarnin biyan Naira dubu dari biyar a matsayin diya wa Fintiri.
Kotun daukaka kara ta fusata kan sanar da sakamakon zaben da shugaban hukumar Hudu Ari ya yi da wuri, inda ta kara da cewa batutuwa marasa hujja sun dabaibaye karar ta Binani.
Kotun ta jaddada cewa matakin da kwamishinan zabe na jihar ya dauka na bayyana Binani a matsayin wanda ta lashe zaben ya sabawa doka.
Wannan hukunci na kotun na yau tabbatar da hukuncin da kotun sharia zaben gwamna ta yanke a ranar 28 ga watan Oktoba inda ta yi watsi da karar da Binani ta shigar.