Sunday, January 5, 2025
Home Muhimman Labarai Shugaban Tinubu ya taya Alhassan Yahaya murnar zabensa shugaban...

Shugaban Tinubu ya taya Alhassan Yahaya murnar zabensa shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa

Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya Alhassan Yahaya murnar zabensa da aka yi a matsayin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) a taron wakilan kasa na kungiyar karo na 8 a Owerri, ranar 27 ga watan Nuwamba, 2024.

Shugaban ya kuma taya sauran sabbin zababbun mambobin kungiyar ta NUJ murna.

Ya yabawa kungiyar da ta shirya zabe ba tare da magudi ba a wurin taron.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na muhimman (Bayanai & Dabaru) ya fitar a ranar Asabar.

Shugaba Tinubu ya ce gagarumar nasarar da Yahaya ya samu, wata shaida ce ta amincewa da ‘ya’yan kungiyar ta NUJ a kan halayensa na shugabanci.

Tinubu ya bayyana fatansa cewa gogewar Alhassan Yahaya, musamman a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kungiyar, zai taimaka matuka yayin da yake jagorantar kungiyar ta yan jaridun.

Shugaban ya jaddada mahimmancin ‘yan jarida su ci gaba da gudanar da ayyukansu bias tanadi na kundin tsarin mulkin kasa tare da kishin kasa, wanda ya dace da hangen nesa da kokarin wadanda suka kafa aikin jarida a Najeriya.

Ya nanata kudurin gwamnatin na tabbatar da samar da kafafen yada labarai masu zaman kansu don karfafa dimokuradiyya da bunkasa ci gaban kasa.

RELATED ARTICLES

An Yabawa Gidauniyar Farindoki Saboda Wanzar Da Zaman Lafiya

An yabawa Gidauniya mai zaman kanta ta Farindoki Foundation dangane da ayyukan wanzar da zaman lafiya, cigaba da hadin kai tsakanin al'umma. Hakimin Billiri da...

Za a gina sabuwar matatar man fetur a Gombe

Hukumomin da ke kula da albarkatun man fetur a Najeriya sun bai wa kamfanin Process Design and Development Limited lasisin gina sabuwar matatar mai...

Hatsari jirgin sama ya sa mataimakin shugaban kasa soke ziyarar sa

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya soke ziyarar sa zuwa taron Shugabannin Gwamnatocin Ƙasashe rainon Ingila (Commonwealth (CHOGM) na 2024 a Samoa bayan da...
- Advertisment -

Most Popular

An Yabawa Gidauniyar Farindoki Saboda Wanzar Da Zaman Lafiya

An yabawa Gidauniya mai zaman kanta ta Farindoki Foundation dangane da ayyukan wanzar da zaman lafiya, cigaba da hadin kai tsakanin al'umma. Hakimin Billiri da...

Shugaban Tinubu ya taya Alhassan Yahaya murnar zabensa shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa

  Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya Alhassan Yahaya murnar zabensa da aka yi a matsayin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) a taron...

Za a gina sabuwar matatar man fetur a Gombe

Hukumomin da ke kula da albarkatun man fetur a Najeriya sun bai wa kamfanin Process Design and Development Limited lasisin gina sabuwar matatar mai...

Hatsari jirgin sama ya sa mataimakin shugaban kasa soke ziyarar sa

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya soke ziyarar sa zuwa taron Shugabannin Gwamnatocin Ƙasashe rainon Ingila (Commonwealth (CHOGM) na 2024 a Samoa bayan da...

Recent Comments