Tuesday, January 7, 2025
Home Muhimman Labarai Tanka ɗauke da man fetur ta yi sanadiyyar kashe sama da mutum...

Tanka ɗauke da man fetur ta yi sanadiyyar kashe sama da mutum 100 a jihar Jigawa

Wata tanka ɗauke da man fetur ta yi sanadiyyar kashe sama da mutum 100 a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya bayan ta faɗi tare da kamawa da wuta.

Babbar jami’ar hukumar kiyaye haɗurra a Jigawa, Aishatu Sa’adu, ta ce zuwa yanzu mutum 104 ne suka mutu sakamakon hatsarin da ya faru ranar Talata da dare.

Da take magana yayin da ta isa wurin da lamarin ya faru a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura, Aisha ta ce wasu mutum 100 sun jikkata.

Tun da farko ta shaida wa BBC cewa ibtila’in ya faru ne bayan da direban tankar ya kauce wa wata babbar mota ɗauke da tumatur.

Hakan ya sa direban tankar ya faɗa gefen titin har kan motar ya rabu da gangar jikinta, lamarin da ya sa fetur ɗin da yake dako ya malale titi da kwatoci a gefen hanyar.

Kakakin rundunar ‘yansanda a Jigawa, DSP Lawan Adam, ya ce ganin haka ne ya sa mutane suka yi dafifi a wurin da lamarin ya faru domin kwasar man da ya zuba a ƙasa bayan sun ci ƙarfin jami’an tsaron da ke korarsu a ƙokarin kauce wa tashin gobara.

Shaidu sun shaida wa BBC cewa tankar ta yi kusan awa biyu tana ci da wuta kafin jami’an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.

Zuwa yanzu ana shirin yin jana’izar mutanen da suka mutu sakamakon fashewar tankar.

Ko a farkon watan Satumban bana, irin wannan ibtila’i ya halaka mutum 59 a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya bayan da wata tankar mai ta yi karo da wata babbar mota ɗauke da fasinjoji da kuma shanu.

Ana yawan samun faruwar hatsarin tankokin mai a Najeriya, musamman saboda rashin kyawun tituna da kuma tuƙin ganganci.

BBC HAUSA

RELATED ARTICLES

An Yabawa Gidauniyar Farindoki Saboda Wanzar Da Zaman Lafiya

An yabawa Gidauniya mai zaman kanta ta Farindoki Foundation dangane da ayyukan wanzar da zaman lafiya, cigaba da hadin kai tsakanin al'umma. Hakimin Billiri da...

Shugaban Tinubu ya taya Alhassan Yahaya murnar zabensa shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa

  Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya Alhassan Yahaya murnar zabensa da aka yi a matsayin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) a taron...

Za a gina sabuwar matatar man fetur a Gombe

Hukumomin da ke kula da albarkatun man fetur a Najeriya sun bai wa kamfanin Process Design and Development Limited lasisin gina sabuwar matatar mai...
- Advertisment -

Most Popular

Hatsari jirgin sama ya sa mataimakin shugaban kasa soke ziyarar sa

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya soke ziyarar sa zuwa taron Shugabannin Gwamnatocin Ƙasashe rainon Ingila (Commonwealth (CHOGM) na 2024 a Samoa bayan da...

Recent Comments