Thursday, September 19, 2024
Home Muhimman Labarai Za A Fara Dandaƙe Masu Yi Wa Yara Fyaɗe

Za A Fara Dandaƙe Masu Yi Wa Yara Fyaɗe

Ministan shari’a na Madagascar ya kare wani sabon kudiri a ranar Juma’a don hukunta masu yiwa kananan yara fyade.

Kungiyar kare hakkin biladama ta Amnesty International dai ta bayyana hukuncin da kudirin ya tanadar a matsayin mara tausayawa.

Majalisar dattawan kasar ta amince da matakin da ya ba da damar yin amfani da sinadarai da tiyata a ranar Laraba domin dandage wadanda a ka samu da laifi bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri’a a farkon wannan watan.

Kungiyar Amnesty International ta bukaci gwamnatin kasar da ta yi watsi da wannan doka da ake shirin yi, tana mai cewa ba za ta magance matsalar fyade ba.

Sai dai ministan shari’a Landy Bolatiana ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa Madagascar “kasa ce mai cin gashin kanta da ke da ‘yancin yin kwaskwarima ga dokokinta”.

Ya zuwa yanzu mafi karancin hukuncin fyade ga yara shi ne daurin shekaru biyar a gidan yari

Kudirin da kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani, ya gabatar da hukuncin dandaka ga masu aikata laifin fyade da aka yi wa duk yara ‘yan kasa da shekara 10”.

RELATED ARTICLES

Kotu ta tabbatar da zaben Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Adamawa bayan ta yi...

Kotu koli ta tabbatar da zaben shugaban kasa Tinubu

A yau Alhamis ne kotun koli ta tabbatar da nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a...

Kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben Tinubu gobe Alhamis

    A gobe  Alhamis, 26 ga Oktoba, 2023 ne dai kotun kolin za ta yanke hukunci kan shari’ar jam’iyyar Labour da dan takararta na shugaban...
- Advertisment -

Most Popular

Za A Fara Dandaƙe Masu Yi Wa Yara Fyaɗe

Ministan shari'a na Madagascar ya kare wani sabon kudiri a ranar Juma'a don hukunta masu yiwa kananan yara fyade. Kungiyar kare hakkin biladama ta ...

Kotu ta tabbatar da zaben Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Adamawa bayan ta yi...

Kotu koli ta tabbatar da zaben shugaban kasa Tinubu

A yau Alhamis ne kotun koli ta tabbatar da nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a...

Kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben Tinubu gobe Alhamis

    A gobe  Alhamis, 26 ga Oktoba, 2023 ne dai kotun kolin za ta yanke hukunci kan shari’ar jam’iyyar Labour da dan takararta na shugaban...

Recent Comments