Hukumomin da ke kula da albarkatun man fetur a Najeriya sun bai wa kamfanin Process Design and Development Limited lasisin gina sabuwar matatar mai a Dole-Wure da ke Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta NMDPRA ta fitar a shafinta na X a ranar Alhamis.
Ana sa ran bayan kammala matatar za ta riƙa fitar da tataccen man fetur kimanin ganga 27,000 a kowace rana.
Process Design and Development Limited kamfani ne na Najeriya wanda aka assasa a Jihar Kano. Kamfanin yana da Lambar Rijista 487883 da ya samu tun a watan Agustan 2003.
A watan Oktobar 2019 ne Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya sanar da gano ɗanyen man fetur a Kogin Kolmani da ke yankin Gongola a Arewa maso Gabashin kasar nan.
Kazalika, NNPC ya ce adadin man da aka gano a yankin na Arewa ya kai munzalin da za a yi cinikayyarsa, lamarin da zai janyo hankalin masu zuba jari daga ƙetare da kuma bunƙasa tattalin arziki da samar da aiki a ƙasar.
A watan Nuwamban 2022 ne tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin fara tonon rijiyoyin mai a yankin da ya haɗa da Jihar Bauchi da Gombe da Yobe gami da Adamawa.
Aminiya