Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da kada ya tsawaita wa’adin ranar 10 ga watan Fabreru na daina karban tsoffin takardun kudaden Naira.
An dai yi ta matsin lamba ga babban bankin kasa daga ‘yan Najeriya da dama da ya kara wa’adin yin musaya da takardun kudi na Naira saboda karancin kudin da aka sake wa fasali na N200, N500, da N1,000.
Tsohon mataimakin shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bukaci CBN da kada ya kara wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu.
Sai dai ya bukaci babban bankin kasa da ya gaggauta yin nazari a kan matakan da aka sanya na tabbatar da cewa an samu wadatuwar sabbin takardun kudi domin rage wahalhalun da ke addabar talakawa a fadin kasar nan, musamman mazauna karkara, wadanda ke bukatar kudi don gudanar da harkokinsu na kasuwancin.
Ya kuma yi zargin cewa ’yan siyasa da ke shirin yin magudi a babban zaben kasar nan na yin zagon-kasa don kara tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudi domin yin magudin zabe.