Thursday, November 14, 2024
Home Muhimman Labarai Kotun koli ta dage ci gaba da shari’ar da ta ke kan...

Kotun koli ta dage ci gaba da shari’ar da ta ke kan sauya wasu takardun kudi

Kotun kolin Najeriya ta dage ci gaba da shari’ar da ta ke kan sauya wasu takardun kudi na naira na babban bankin Najeriya CBN zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu domin sauraron kararrakin da jihohi 10 suka hada.
Kotun kolin da ta saurari karar a ranar Larabar ta cika makil da wasu manyan lauyoyi da sauran gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi, Nasir El-Rufai da Yahaya Bello.
A zaman da ya gabata, Kotun ta dakatar da aiwatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na CBN daga janye takardar kudi ta N200, N500 da N1,000.
Jihohin Zamfara da Kogi da kuma Kaduna ne suka shigar da karar gwamnatin tarayya da kuma babban bankin kasa CBN.
Sauran jihohin da suka hada da Neja, Kano, Ondo, Ekiti, su ma sun nemi a shigar da su cikin masu karar CBN da gwamnatin tarayya.
An fara zaman kotun inda mai shari’a John Okoro ya jagoranci kwamitin mutum bakwai na alkalan kotun.
Jihar Legas, ta hannun babban mai shari’a, Moyosore Onigbanjo, ita ma ta nemi a shigar da ita cikin kara.
Jihar Bayelsa, karkashin jagorancin laiya Damian Dodo, ita ma ta nemi a shigar da ita cikin masu kara Hakazalika, Jihar Edo ta nemi a shigar da ita.

RELATED ARTICLES

Hatsari jirgin sama ya sa mataimakin shugaban kasa soke ziyarar sa

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya soke ziyarar sa zuwa taron Shugabannin Gwamnatocin Ƙasashe rainon Ingila (Commonwealth (CHOGM) na 2024 a Samoa bayan da...

Tanka ɗauke da man fetur ta yi sanadiyyar kashe sama da mutum 100 a jihar Jigawa

Wata tanka ɗauke da man fetur ta yi sanadiyyar kashe sama da mutum 100 a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya bayan ta faɗi...

Kungiyar Ƴanjarida Ta ƙasa Ta karrama Gwamnan Jihar Kano

Tawaga daga kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Kwamared Chris Isiguzo, sun karrama gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf...
- Advertisment -

Most Popular

Za A Fara Dandaƙe Masu Yi Wa Yara Fyaɗe

Ministan shari'a na Madagascar ya kare wani sabon kudiri a ranar Juma'a don hukunta masu yiwa kananan yara fyade. Kungiyar kare hakkin biladama ta ...

Recent Comments