Thursday, September 19, 2024
Home Uncategorized Mataikin shugaban kasa Ya Mutu a Indiya

Mataikin shugaban kasa Ya Mutu a Indiya

Mataimakin Shugaban Kasar Gambiya, Badara Joof, ya rasu a kasar Indiya.

Shugaban Kasar, Adama Barrow ne ya sanar da rasuwar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter da safiyar Laraba.

To sai dai sanarwar ba ta bayyana lokacin da ya rasu ba, da kuma ko ya je ganin likita ne kafin rasuwar tasa.

Badara Joof dai ya yi karatunsa a Jami’ar Bristol da kuma digirinsa na biyu a fannin Adabin Turanci daga Jami’ar Landan da kuma a fannin Tattalin Arziki daga Jami’ar Bath.

Ya fara aikin gwamnati ne a matsayin malamin Turanci a Kwalejin Gambiya.

A shekarar 2014, Bankin Duniya ya nada Badara a matsayin kwararren jami’in ilimi a kasar Senegal.

A ranar 22 ga watan Fabrairun 2017, Shugaba Adama Barrow ya nada marigayin a matsayin Ministan Ilimi mai Zurfi, Bincike da Kimiyya da Fasaha.

RELATED ARTICLES

NNPC ya nemi afuwan ‘yan Najeriya kan karancin man fetur

Shugaban Kamfanin mai na kasa, NNPC ya bai wa 'yan Najeriya hakuri kan matsin da suka sake tsintar kansu sakamakon karancin man fetur. Shugaban kamfanin...

Wani Mutum Ya kai ƙarar Hadiza Gabon Saboda Ta ƙi Auransa

Wani ma’aikacin gwamnati Bala Musa mai shekaru 48 a duniya a ranar Litinin ya maka wata jarumar fina-finan Kannywood Hadiza Gabon a...
- Advertisment -

Most Popular

Za A Fara Dandaƙe Masu Yi Wa Yara Fyaɗe

Ministan shari'a na Madagascar ya kare wani sabon kudiri a ranar Juma'a don hukunta masu yiwa kananan yara fyade. Kungiyar kare hakkin biladama ta ...

Kotu ta tabbatar da zaben Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Adamawa bayan ta yi...

Kotu koli ta tabbatar da zaben shugaban kasa Tinubu

A yau Alhamis ne kotun koli ta tabbatar da nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a...

Kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben Tinubu gobe Alhamis

    A gobe  Alhamis, 26 ga Oktoba, 2023 ne dai kotun kolin za ta yanke hukunci kan shari’ar jam’iyyar Labour da dan takararta na shugaban...

Recent Comments