Ofishin yaƙin neman neman zaben ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar APC Bola Ahmed Tinubu ya ca ya lura da wasu shafukan labarai na bogi musamman a Facebook da ke yaɗa wani labarin ƙarya da yarfe irin na siyasa wanda ke rawaito cewa wai an kama wasu motoci da kuɗaɗe mallaki ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗaukr da a hannu Abdulaziz Abdulaziz, mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Sanarwar ta ce wannan magana ƙarya ce tsagwaronta wanda maƙiya suka shirya domin bata sunan Alhaji Ahmed Bola Tinubu.
“Abin lura a nan shi ne babu wata madogara da su waɗannan masu yaɗa labarun ƙarya suka dogara da ita wajen rawaito wannan magana ta bogi.”
“Muna Jan hankali mutane da su lura da cewa a kwanakin da suka rage mana kafin shiga zaɓe ƴan siyasa marasa tsoron Allah da dama za su yi ta Ƙoƙarin yaɗa labaran ƙarya da sharri domin ɓata sunan abokan hamayyar su da suke ganin cewa ba za su iya kayarda da su a akwatin zaɓe ba sai sun haɗa da ƙarya da sharri domin ɓata musu suna”, a cewar sanarwar.
“Ɗan takarar jam’iyyar APC, Jabagan Borgu ya sha faɗar cewa shi bai yarda da yin sharri ko yarfen siyasa ba domin ba sahihiyar hanya ce ta cin zaɓe ba. Abinda muka dogara da shi shi ne a bar mutane su yi zaɓin ɗan takarar da suka ga ya dace kuma yana da ƙwarewar aiki da zai iya kawowa ƙasa cigaba, ba tare da an bi haramtaciyyar hanya ba wajen ru&ar da tunanin masu zaɓe” inji sanarwar.
Sanarwa ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da labarin a ta bayyana da na bogi marar hujja wanda wasu da ta kira maƙiya kuma marasa son zaman lafiya zuka ƙirƙira.