Tuesday, December 31, 2024
Home Siyasa Ofishin yaƙin neman zaɓen Tinubu ya ce a na yaɗa labaran...

Ofishin yaƙin neman zaɓen Tinubu ya ce a na yaɗa labaran ƙarya kan ɗan takaran

Ofishin yaƙin neman neman zaben ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar APC Bola Ahmed Tinubu ya ca ya lura da wasu shafukan labarai na bogi musamman a Facebook da ke yaɗa wani labarin ƙarya da yarfe irin na siyasa wanda ke rawaito cewa wai an kama wasu motoci da kuɗaɗe mallaki ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗaukr da a hannu Abdulaziz Abdulaziz, mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Sanarwar ta ce wannan magana ƙarya ce tsagwaronta wanda maƙiya suka shirya domin bata sunan Alhaji Ahmed Bola Tinubu.

“Abin lura a nan shi ne babu wata madogara da su waɗannan masu yaɗa labarun ƙarya suka dogara da ita wajen rawaito wannan magana ta bogi.”

“Muna Jan hankali mutane da su lura da cewa a kwanakin da suka rage mana kafin shiga zaɓe ƴan siyasa marasa tsoron Allah da dama za su yi ta Ƙoƙarin yaɗa labaran ƙarya da sharri domin ɓata sunan abokan hamayyar su da suke ganin cewa ba za su iya kayarda da su a akwatin zaɓe ba sai sun haɗa da ƙarya da sharri domin ɓata musu suna”, a cewar sanarwar.

“Ɗan takarar jam’iyyar APC, Jabagan Borgu ya sha faɗar cewa shi bai yarda da yin sharri ko yarfen siyasa ba domin ba sahihiyar hanya ce ta cin zaɓe ba. Abinda muka dogara da shi shi ne a bar mutane su yi zaɓin ɗan takarar da suka ga ya dace kuma yana da ƙwarewar aiki da zai iya kawowa ƙasa cigaba, ba tare da an bi haramtaciyyar hanya ba wajen ru&ar da tunanin masu zaɓe” inji sanarwar.

Sanarwa ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da labarin a ta bayyana da na bogi marar hujja wanda wasu da ta kira maƙiya kuma marasa son zaman lafiya zuka ƙirƙira.

RELATED ARTICLES

Jami’yar APC ta Dakatar Da Ɗan takarar Gwamna Da Na Sanata A Taraba

Jam'iyyar APC a jihar Taraba ta kori ɗan takararta na gwamnan jihar a zaɓen 2023 da aka kammala David Sabo Kente kan zargin yi...

Gwamnoni shida sun gaza cin zabe don tsallakawa majalisar dattawa

Akalla gwamnoni shida masu barin gado sun gaza a yunkurinsu na tsallakawa majalisar dattawan Najeriya bayan wa’adinsu biyu na shekara takwas. Gwamnonin da ke barin...

Kotu Ta Kori karar Neman Hana Inuwa Takarar Gwaman Gombe

Kotu Ta Kori karar Da Ke Neman Hana Inuwa Takarar Gwaman Gombe A jiya ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi...
- Advertisment -

Most Popular

An Yabawa Gidauniyar Farindoki Saboda Wanzar Da Zaman Lafiya

An yabawa Gidauniya mai zaman kanta ta Farindoki Foundation dangane da ayyukan wanzar da zaman lafiya, cigaba da hadin kai tsakanin al'umma. Hakimin Billiri da...

Shugaban Tinubu ya taya Alhassan Yahaya murnar zabensa shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa

  Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya Alhassan Yahaya murnar zabensa da aka yi a matsayin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) a taron...

Za a gina sabuwar matatar man fetur a Gombe

Hukumomin da ke kula da albarkatun man fetur a Najeriya sun bai wa kamfanin Process Design and Development Limited lasisin gina sabuwar matatar mai...

Hatsari jirgin sama ya sa mataimakin shugaban kasa soke ziyarar sa

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya soke ziyarar sa zuwa taron Shugabannin Gwamnatocin Ƙasashe rainon Ingila (Commonwealth (CHOGM) na 2024 a Samoa bayan da...

Recent Comments