Thursday, November 14, 2024
Home Uncategorized Wani Mutum Ya kai ƙarar Hadiza Gabon Saboda Ta ƙi Auransa

Wani Mutum Ya kai ƙarar Hadiza Gabon Saboda Ta ƙi Auransa

Wani ma’aikacin gwamnati Bala Musa mai shekaru 48 a duniya a ranar Litinin ya maka wata jarumar fina-finan Kannywood Hadiza Gabon a gaban kotun shari’a da ke Kaduna saboda ta ki aurensa.

Wanda ya shigar da karar ya shaidawa kotu cewa yana da alaka da jarumar kuma ta yi alkawarin aurensa.

Musa ya shaida wa kotun cewa, “Ya zuwa yanzu na kashe mata N396,000. Duk lokacin da ta nemi kudi ina ba ta ba tare da bata lokaci ba tare da fatan za mu yi aure.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an fara sauraren karar ne a ranar 23 ga watan Mayu, amma Hadiza ba ta kotu.

Lauya wanda a ke kara Kabir ya roki kotun da ta kara masa lokaci domin gabatar da wanda yake karewa a kotu.

Khadi, Malam Rilwanu Kyaudai, ya dage zaman zuwa ranar 13 ga watan Yuni.

RELATED ARTICLES

NNPC ya nemi afuwan ‘yan Najeriya kan karancin man fetur

Shugaban Kamfanin mai na kasa, NNPC ya bai wa 'yan Najeriya hakuri kan matsin da suka sake tsintar kansu sakamakon karancin man fetur. Shugaban kamfanin...

Mataikin shugaban kasa Ya Mutu a Indiya

Mataimakin Shugaban Kasar Gambiya, Badara Joof, ya rasu a kasar Indiya. Shugaban Kasar, Adama Barrow ne ya sanar da...
- Advertisment -

Most Popular

Hatsari jirgin sama ya sa mataimakin shugaban kasa soke ziyarar sa

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya soke ziyarar sa zuwa taron Shugabannin Gwamnatocin Ƙasashe rainon Ingila (Commonwealth (CHOGM) na 2024 a Samoa bayan da...

Tanka ɗauke da man fetur ta yi sanadiyyar kashe sama da mutum 100 a jihar Jigawa

Wata tanka ɗauke da man fetur ta yi sanadiyyar kashe sama da mutum 100 a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya bayan ta faɗi...

Kungiyar Ƴanjarida Ta ƙasa Ta karrama Gwamnan Jihar Kano

Tawaga daga kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Kwamared Chris Isiguzo, sun karrama gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf...

Za A Fara Dandaƙe Masu Yi Wa Yara Fyaɗe

Ministan shari'a na Madagascar ya kare wani sabon kudiri a ranar Juma'a don hukunta masu yiwa kananan yara fyade. Kungiyar kare hakkin biladama ta ...

Recent Comments