Thursday, September 19, 2024
Home Kiwon Lafiya Zazzabin Lassa Ya kashe Mutum 13 a Jihar Edo.

Zazzabin Lassa Ya kashe Mutum 13 a Jihar Edo.

Akalla mutum 13 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 115 suka harbu da cutar zazzabin Lassa a Jihar Edo.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Farfesa Akoria Obehi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Benin, babban birnin Jihar.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta zage damtse wajen ganin ta dakile yaduwar cutar a fadin jihohin da cutar da barke.

Ya ce sun samu karin mutum takwas da suka kamu da cutar, wanda adadinsu ya kai 115 zuwa yanzu kuma suna Asibitin Koyarwa na Irrua inda suke karbar magani.

Akoria, ya bukaci al’ummar jihar da suka fuskanci matsanancin ciwon kai, zazzabi ko amai, da su garzaya asibitin da ke kusa da su don neman daukin likitoci.

Yanzu haka dai cutar zazzabin Lassa ta bulla a Jihohin Kano da Bauchi da Gombe da Filato da Legas da sauransu.

Sai dai Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka (NCDC), ta ce tana aiki kafada da kafada da gwamnatocin Jihohi don dakile cutar.

RELATED ARTICLES
- Advertisment -

Most Popular

Za A Fara Dandaƙe Masu Yi Wa Yara Fyaɗe

Ministan shari'a na Madagascar ya kare wani sabon kudiri a ranar Juma'a don hukunta masu yiwa kananan yara fyade. Kungiyar kare hakkin biladama ta ...

Kotu ta tabbatar da zaben Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Adamawa bayan ta yi...

Kotu koli ta tabbatar da zaben shugaban kasa Tinubu

A yau Alhamis ne kotun koli ta tabbatar da nasarar da shugaba Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a...

Kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben Tinubu gobe Alhamis

    A gobe  Alhamis, 26 ga Oktoba, 2023 ne dai kotun kolin za ta yanke hukunci kan shari’ar jam’iyyar Labour da dan takararta na shugaban...

Recent Comments